Friday

Home Dakarun Jam'iyyar APC 6 Da Ke kokarin Dusashe Hasken Shugaba Buhari a Zaben 2019
Shugaba Buhari na fama da kalubalen lafiya
- Tsofin Gwamnonin da wasu masu ci a jam'iyyar
APC na burin takarar shugabancin kasa
Ganin yadda Shugaban Kasa Muhammadu
Buhari ke fama da kalubalen Lafiya, akwai
yiwuwar bazai kara takarar shugabancin
kasa ba a zaben sherar 2019.

Hakan ya sa wasu daga cikin dakarun
jam'iyyar APC mai mulki kokarin maya
gurbin shugaba Muhammadu Buharin a
kakar zabe ta 2019.
Cikin wadan da ake hasashen za su yi takarar kujerar Shugaban Kasa a Jam'iyyar ta APC sun hada da tsofin gwamnoni 5 da tsohonmataimakin shugaban kasa guda 1.


1.Engr. Rabiu Musa Kwankwaso

A zaben da aka yi na Shekarar 2015,
Kwankwaso ne ya zo na biyu a zaben fitar da gwani da jam'iyyar APC ta shirya kuma har yanzu, Sanatan kuma tsohon gwamnan na
jihar Kano, na harin kujerar shugaban kasa azabe mai zuwa.

2. Dr. Bukola Saraki

Tsohon gwaman jihar Kwara karkashin
jam'iyyar PDP, yanzu haka Saraki dan
jam'iyyar APC kuma shine shugaban
majalisar dattawa ta kasa.

3.Atiku Abubakar

Tsohon dan Jam'iyyar PDP da ACN kafin daga bisani a watan Febereru na shekarar 2014 ya kara canja sheka zuwa Jam'iyyar APC, Atiku Abubakar, tsohon maiamakin shugaban kasa, Obasanjo, zai cika Shekarar 72 da haihuwa aduniya a 2019.

4. Mallam Nasir el'rufa'i.

Tsohon ministan Abuja karkashin mulkin
PDP/Obasanjo kafin ya tsallaka zuwa
jam'iyyar APC inda ya lashe zaben takarar
Gwamnan Kaduna da aka yi a Shekarar 2015.

5.Rochas Anayo Okorocha.

Hamshakin dan kasuwa mai yawan taimako,
jigo ne na 'yan siyasa a jihar Imo inda ya ke gwamna tun Shekarar 2011 har yanzu.

6. Ibrahim Kashim Shettima.

Dan Siyasa ne Kwararre, ya zama Gwamna
ne a jihar Borno a jamiyyar ANPP a karo na farko a shekarar 2011 kafin daga baya ya koma jam'iyyar APC inda ya kuma lashe
zaben gwamnan a karo na biyu a 2015.
No comments:
Write Comments