Wednesday

Home › › Dalilin da yasa naki amincewa in fito 'yar madigo - Rahma Sadau
Korarriyar shahararriyar jarumar fina-finan nan na Kannywood a da yanzu kuma hadda fina- finan kudu Rahma Sadau ta bayyana cewa an sota fito a wani fim din ta na fina-finan kudu a matsayin yar madigo amma sai ta ki yadda saboda la'akari da daga inda ta fito watau arewa.

Jarumar ta bayyana hakan ne a cikin wata
fira da tayi da jaridar The Guardian a
karshen makon jiya inda kuma ta bayyana
cewa tayi haka ne kawai bisa la'akari da
daga inda ta taso da kuma martaba al'ada daaddinin yankin arewa.

NAIJ.com kuma dai ta samu cewa da take
tsokaci game da korar ta da kungiyar fina- finai tayi, Rahma Sadau tace ita wannan korar ma gaba ta kaita don kuwa yanzu idon ta ya kara budewa kuma ta kara samun wasu damammaki na gudanar da sana'arta a dukkan fadin duniya.

Haka nan kuma jarumar ta bayyana
rungumar da tayiwa mawaki ClassiQ da tayi
sanadiyyar korar tata a matsayin bangaren
aikin ta da bai kamata a tsangwameta ba
game da hakan.

Daga karshe ne kuma sai jarumar ta kara
jawo hankalin mutane da cewa shifa tsoron
Allah a zuciya yake don haka ba dai dai baneba a rika yi mata kallon 'yar iska don kawai tana sana'ar ta.KU KALLI WASU VIDEOS NATA DA TA FITAR A BAYA BAYANNAN.


No comments:
Write Comments