Friday

Home Dutsen Florence na ci gaba da kusantar duniya.
Masanan Kimiyya sun ce dutsen zai wuce ta kusa da duniya a wannan rana.
Masanan Kimiyya sun ce dutsen zai wuce ta kusa da duniya a wannan rana. Dutsen zai wuce ta kusa da duniya da nisan kilomita miliyan 7. Kuma wannan adadi ya ninka sau 18 sama da adadin tafiyar da ke tsakanin duniya da wata. Hukumar Bincike kan sararin samaniya ta Amurka NASA ta bayyana cewa, wannan ne karo na farko da wani abu mafi girma ya wuce ta kusa da duniya. Masanan Kimiyya sun ce sun tanadi na'urori don shaida yadda Fılrence zai wuce ta kusa da duniyar. Za a bibiyi wucewar dutsen daga kasashen Niyuzelan da Ostireliya. Bayan Florence wasu abubuwa za su ci gaba da wuce wa ta kusa da duniyar tamu. NASA dai ta ce, a watan Oktoba ne dutse mafi girma zai wuce ta kusa da duniyar tamu. Ku cigaba da kasancewa damu domin samun videon.
No comments:
Write Comments