Wednesday

Home › › Gwamnatin Buhari ta sai wa Nnamdi Kanu gida aLandan — Uwazuruike
Wanda ya samar da kungiyar neman 'yancin
kasar Biafra (MASSOB), Ralph Uwazuruike,
ya ce gwamnatin Najeriya ta riga ta siye mai jagorantar kwatar kasar Ibo, Nnmadi Kanu.
Ya ce har sun sai masa gida a Birnin Landan.


Uwazuruike ya fadi hake ne a tattaunawa da aka yi da shi a mujallar Interview .
Ya ce, "Gwamnatin Buhari ta tunkari Kanu da tukwicin da ba kowa bane zai iya kin karba ba don ya yiwa neman 'yancin Biafra zabon kasa.
Gaskiyar lamarin zai fito kome daren dadewa.
"Sanda Kanu ya ce kar a fita ayi zabe a Jihar Anambra a watan Nuwamba na bara
makarkasa ce don jam'iyyar APC ta samu
kujerar gwamna a jihar.
"Kanu bai san bambancin zaben kujerar siyasa ba da zaben neman 'yanci. Kuma ya ingizo 'yan Ibo da kalaman tarzoma don su nuna zasu kwaci Baifra ta karfi da yaji. Zai janyo 'yan Ibon da ke zama a Arewa su rasa rayukan su a banza da wofi."


Uwazuruike ya ce 'yan Ibo bai kamata suna
koyi da Kanu ba. In ana neman 'yancin kasa ba da fada ake kwata ba. Maganganu za ayi ta yi na hankali har sai an karba.
Ya ce Kanu ya kamata yayi koyi da Mahatma
Ghandi ko Martin Luther Jr.
No comments:
Write Comments