Tuesday

Home Gwamnatin Buhari ta Tona Asirin "yan kungiyar IPOB
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta tona asirin Kungiyar IPOB ta Biyafara da yunkurin amfani da bidiyoyin karya wajen rudar al'ummar Duniya.
Gwamnatin Tarayya ta bankado furofagandar 'Yan Biyafara Ministan yada labarai Lai Mohammed Ministan yada labarai na kasa watau Lai Mohammed ya bayyana wannan a wata hira da yayi da wasu a Legas. Lai Mohammed yace 'Yan Biyafarar na yada bidiyoyi na jabu na wasu kashe-kashe da aka yi a wasu kasashen Afrika a matsayin irin kisan gillar da Sojojin Najeriya ke yi wa mabiya Biyafarar. Ministan yace abu na gaba yanzu shi ne ayi kokarin dakile irin karyar da 'Yan Biyafaran ke yadawa a Duniya. Lai yace 'Yan Kungiyar na kokarin amfani da furofaganda da karfi da yaji domin jawo hankalin Shugabanni da Majalisun Duniya wanda har wasu sun fara ruduwa da wannan. Ministan ya kara kira ga 'Yan jarida da su guji yada irin wadannan furofaganda na banza ya kuma kara nanata cewa wasu 'yan adawa ne ke marawa 'Yan Biyafara masu tada kafar baya.
No comments:
Write Comments