Wednesday

Home › › Har na fara tunanin ƙkasar da zan tafi gudun hijira–inji Buhari, karanta
Buhari ya danganta tunanin barin kasar ne
da halin matsin tattalin arziki daya tarar da kasar nan a ciki lokacin daya karbi ragamar mulkin kasar nan, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito.

Shugaban kasa yayi wannan jawabi be a
ranar daya karbi bakoncin sarakunan
gargajiyan Najeriya a fadar shugaban kasa
dake Abuja,inda ya koka kan yadda wasu
gwamnoni suka kashe kudaden bashin Paris
daya biya jihohi, musamman yadda wasu
suka gagara biyan albashi da fansho.

Buhari da sarakunan Tawagar Sarakunan sun kawo ziyarar ne a karkashin jagorancin mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Sa’ada Abubakar da Sarkin Ife, Oba Enitan Ogunwusi.


“Mun ci sa’a a bara da bana an samu ruwan
sama mai albarka, da ba dan haka ba kuwa,
har na fara tunanin kasar da zan ruga.

Amma cikin ikon Allah sai albarkun gona suka yi kyau, dole mu gode ma Allah don da an samu matsaloli da dama a kasar.” Inji Buhari.
Shugaba Buhari ya koka kan rashin biyan
albashin ma’aikata a wasu jihohin kasar nan,
“Ina sane da matsalolin Najeriya, akwai yan Najeriya da basu samu albashi ba tsawon
watanni shida, don haka nake rokon yan
Najeriya dasu biya su.”

A nasa jawabin, Sarkin Musulmi yace sun
kawo ma Buhari ziyarar ne don nuna
godiyarsu ga Allah daya bashi lafiya bayan jinyar da yayi mai tsawo, sa’annan kuma don su shawarce shi daya dage wajen tunkarar kalubalen mulki.
No comments:
Write Comments