Saturday

Home Jagoran IPOB Nnamdi-Kanu ya garzaya kotu.
(Nnamdi-Kanu) Kungiyar IPOB mai fafutikar kafa jamhuriyar Biafra a Najeriya ta kalubalanci umarnin kotun da ya ayyanata a matsayin kungiyar ta'addanci.

Lauyan kungiyar, Ifeanyi Ejiofor, ya shaida wa BBC cewa kungiyar ta shigar da kara a kotu domin kalubalantar matakin da gwamnatin Najeriya.

Takardar karar wadda kungiyar ta shigar a ranar Juma'a, ta ce IPOB ba ta kaunar tashin hankali.

Ta ce saboda haka hukuncin da wata kotun tarayya da ke Abuja ta yanke na ayyanata a matsayin kungiyar ta'addanci "ya ci karo da doka."

Har ila yau Mista Ejiofor ya ce ba a yi wa Kanu adalci ba domin bai halarci zaman da kotu ta yi kafin a ayyana kungiyarsa a matsayin ta ta'adda ba.

A ranar Laraba ne dai gwamantin Najeriya ta samu hukuncin kotu da ya ayyana IPOB a matsayin kungiyar ta'adda.

Hakazalika a ranar Laraba rundunar sojin saman kasar ta shiga aikin dakile tashin hankali a kudu maso gabashin Najeriya mai suna 'Operation Python Dance II.'

A ranar Litinin tawagar gwamnonin arewacin Najeriya, suka yi wani rangadin shiyyoyin kudu maso gabas da kudu maso kudancin kasar, a wani kokari na shawa kan rikicin.

A baya-bayan nan dai rikicin kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra a yankin ya yi kamari. Source: bbchausa
No comments:
Write Comments