Monday

Home › › Koriya ta Arewa mai samar da makaman nukiliya tayiwa nigeria gargadi.
An gargadi ‘yan Najeriya da su daina yin izgilanci ga shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong-Un ko kuma su dandana kudarsu.

A wani shafin twitter mai dauke da suna Jamhuriyar Demokradiyyar Al’umar Koriya ta Arewa DPRK. Amma shafin ba ya dauke da alamartabbatar da ingancinsa da Kamfanin Twitter ke samarwa.
Sanarwar da shafin ya fitar ta ce “Ana gargadar marasa kunya ‘yan Najeriya da su daina yin izgilanci da kalaman raini ga shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-Un ko kuma su dandana kudarsu.

Koriya ta Arewa dai na yi wa duniya barazana game da makaman Nukiliya da ta ke samarwa musamman ma bam din Hydrogen da ta gwada harba wa wanda ta samar kuma ta ce ya fi bam din Atom hatsari.
Shugabannin duniya dai sun soki Koriya ta Arewa game da wannan abu da ta ke na barazanar tsaro ga duniya baki daya.
No comments:
Write Comments