Saturday

Home Koriya ta Arewa ta sake barazanar za ta gwada harba bam din Hydrogen

Alakar Koriya ta Arewa da Amurka na ci gaba da lalace wa inda bayan kalaman da Trump ya yi a zauren Majalisar Dinkin Duniya ya sanya Koriyan sake barazanar gwada harba bam din Hydrogen mai hatsari.

A yayin atron Majalisar Dinkin Duniya ne Trump ya ce, idan ta kama su shafe Koriya ta Arewa daga ban kasa to za su yi hakan.
Koriyan dai ba ta yi sanya ba wajen mayar da martani inda ministan harkokin wajenta ya ce, idan fa ba a kyale su ba to za su sake gwada harba bam din Hydrogen wanda babu irinsa a duniya.

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-Un ya ce, za su iya daukar kowanne irin mataki don magance Amurka.

{trt.net.tr hausa}
No comments:
Write Comments