Sunday

Home Labarin cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai tafi Amurka karyace kawai - Lai Mohammed


Ministan Labarai da al'adu ya karyata
rahoton zuwan Buhari Amurka gobe.
Ministan yace wannan labari ba gaskiya
bane a wani jawabi da aka saki a jihar Legas.
Da safiyan yau mun bada labarin cewa
shugaba Buhari na shirin tafiya Amurka
gobe, 4 ga watan Satumba, 2017.

Wannan ziyara da shugaban kasan Najeriya
zai kai bisa ga wata goron gayyata da
shugaban kasan Amurka Donald Trump ya
aiko masa da shi ne tun wata Fabrairun
wannan shekarar.

Amma kamar yadda muka sani lokacin ya fara rashin lafiya.

Shugaba Muhammadu Buhari zai tafi Amurka
Game da cewar jaridar Sahara Reporters,
shugaba Buhari bar gida Daura misalign
karfe 9:15 na safe a jirgi mai saukar angulu zuwa filin jirgin saman jihar Katsina inda zai tashi misalign karfe 10 na safe zuwa Amurka.

Wata majiya a fadar shugaban kasa ta
bayyana cewa abinda aka shirya a da shine
shugaba Buhari ya hada tafiyar da taron
gangamin majalisar dinkin duniya da za’ayi ranan 21 zuwa 25 na watan Satumban 2017.
Amma wata majiya na cewa da alamun akwai
kishin-kishin jinya a cikin tafiyar.
No comments:
Write Comments