Thursday

Home Miji ya bukaci a raba aurensa da matarsa matsafiya, karanta abinda take masa
Yaga uwar bari: Mata ta matsafiya ce, tana ɓacewa a duk lokacin data gadama, a raba mu kawai.

Wani mutum dan jihar Legas, Olarenwaju Moruf ya bayyana ma alkalin kotun gargajiya dake Igando cewa matarsa matsafiya ce, don har tana bacewa tana dawowa, inda ya bukaci a raba auren nasu.

An yi wannan shari’a ne a ranar Alhaimis 14 ga watan Satumba, a gaban alkali
Adegboyega Omilola, inda Moruf ya shaida
ma Kotu cewa bawa bukata cigaba da zama
da matarsa Fatima, wanda suka kwashe
shekaru 17 a tare.

“Akwai ranar da mata ta ta bace tun daga
jhar Legas, sai na ganta a Arewa a dakin Otel dina lokacin da naje neman aiki, a lokacin da nayi ihu sai ta bace. Matar nan na zuwa min a duk lokacin da wani abin alheri ya same ni.

“Duk inda naje neman magani, sai a tabbatar min cewa mata tace matsalar rayuwata, a takaice dai matsafiya ce.”
Inji Moruf.

Moruf yace ya taba kama matarsa ta shirya
taron matsafa a gidansu, cikinsu har da wani karamin yaro, wanda an san mahaifin,
gawurtaccen matsafi ne.
Sai dai a nata bangaren, Fatima ta musanta zarge zargen, inda tace ita fa ba matsafiya bace, “Bani da hannu cikin matsalolin mijina, ni musulman kwarai ce.” Inji ta, sa’annan taroki kotu da kada ta kashe auren.

Daga karshe sai alkali Adegboyega ya dage
sauraron karar zuwa ranar 2 ga watan
Nuwamba don cigaba da sauraron karar.

Naij.com/Hausa
No comments:
Write Comments