Wednesday

Home Muhimman Jawabai 5 Na shugaba Muhd Buhari A Taron Majalissar Dinkin Duniya.
Jawabin shugaba Muhammadu Buhari a taron majalisar dinkin duniya.

Jawabin shugaba Muhammadu Buhari a taron majalisar dinkin duniya.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi jawabai a madadin Kasar najeriya baki daya a taron majalisar dinkin duniya,

1. Batun Nukiliyar kasar Iran, Yarjejeniya akan sauye sauye yanayi na na Farisa da hatsaniyar nukiliyar kasar Koriya ta Arewa

2. Yabawa majalisar dinkin duniya akan rawar da ta taka wajen bayar da matsugunni ga 'yan gudun hijira da yakin kasar Siriya, Iraq da Afgahanistan ya yi ma su sanadiyar zamantakewar su da muhallansu.


3. Godiya ga gwamnatin Jamhuriyyar kasar Jamus karkashin jagorancin Angela Merkel da kuma gwamnatocin kasar Italiya, Girka, Turkey wajen taimakawa dubunnan 'yan gudun hijira.

4. Ya jinjinawa kasashen duniya da al'ummominsu wajen jajintawa, taimakawa da goyon bayan nahiyyar mu da al'ummominmu da yankin tafkin Chadi akan barazanar ta'addancin Al Qa'ida da Boko Haram.

5. Jajintawa da nuna damuwarsa akan rashin kare 'yancin ɗan adam rikicin Gabas ta tsakiya, da kuma wahalhalun Falasdinawa da na Gaza. Akwai rikicin kasar Yemen da kuma na kwana-kwanan nan na kasar Myanmar. Shugaba Buhari ya musalta rikicin Myanmar da abin da ya faru a kasar Bosnia a shekarar 1995 da kuma kasar Rwanda a shekarar 1994.
No comments:
Write Comments