Monday

Home Sunan Allah Ya Bayyana A jikin Tsokar Naman Layya


dan kasar Najeriya ya yi gamo da abin
al'ajabi, yayin da sunan Allah mai girma ya
bayyana a jikin wata tsokar nama ta ragon
layya da suka yanka a bikin babbar sallar da
ta gabata kwanaki kadan.
Abin Al'ajabi: Sunan Allah ya bayyana a jikin naman
ragon layya
Abin Al'ajabi: Sunan Allah ya bayyana a jikin naman
ragon layya
Abin Al'ajabi: Sunan Allah ya bayyana a jikin naman
ragon layya
Shi dai wannan bawan Allah, wanda yake
amfani da sunan Abdullateeph Da Prince
Adeyemie a shafin sa na dandalin sada
zumunta, ya bayyana cewa, yayi gamo da
sunan Allah ne a jikin soyayyar tsokar nama
ta ragon su na layya, inda ya dauki hotuna
kuma ya watsa a shafin sa na Facebook.

Ya kuma rubuta a shafin na sa cewa:
"Wallahi na shaida babu wani sarki sai Allah.
Na saba jin zantuttukan bayyanar sunan
Allah akan abubuwa da dama. Amma yau, na
tabbatar da kaina."
"Sunan Allah ya bayyana a jikin wata tsokar
nama ta ragon mu na layya bayan an soya,
kuma wannan shi yake nuna kadaitakar Allah
da kuma buwayarsa. Sunan ya bayyana a jikin
tsokoki biyu. #AllahuAkbar"
No comments:
Write Comments