Wednesday

Home › › [Video] Matasa majiya ƙkarfi sun jibgi tsohuwa mai shekaru 70 har lahira

Yansandan jihar Bauchi sun cika hannu da
wasu mutane 4 da suka lallasa wata mata har ta mutu sakamakon zargin ta da maita a wani kauyen Bauchi, Doka.
Kaakakin rundunar, ASP Kamal Mohammed
ya bayyana haka a ranar Talata 12 ga watan Satumba, inda yace wanann lamarin ya auku ne a satin data gabata, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito Kaakakin yana
fadin matasan sun kama matar ne mai suna
Liyatu Michael da wata kawarta mai suna
Keziya, inda suka kulle su a cikin wani daki, suka dinga jibgarsu.

Wasu matasa Daga bisani ne Yansanda suka samu rahoton lamarin, indu suka garzaya suka kama matasan su hudu, yayin da sauran kuma suka cika wandonsu da iska, sa’annan suka tafi da gawar matar.

Majiyar tace matsalar ta taso ne a lokacin da matan su biyu suka tabbatar da cewa su mayu ne, kuma sun eke janyo bala’o’i daban-daban a kauyen nasu.

(Ku Kalli Videos)
No comments:
Write Comments