Thursday

Home (video):Sojoji sun mayar da martani akan bidiyon da ya nuna ana cin zarafin yan kungiyan IPOB
An fara bicike akan bidiyon kuma za a bayyana ma al'umma sakamakon binciken.

Bidiyon ya nuna sojoji suna dukan yan kungiyan IPOB da bulala kuma sun sa wasu wanka da shan ruwan kwata.

Rundunar sojojin Najeriya ta fara binciken wani bidiyon da ke yawo a shafikan sa da zumunta da ya nuna sojoji suna cin zarafin yan kungiyan IPOB.

Bidiyon mai tsawon minit 3, ya nuna tutar
Biyafara a kasa da muntane a kwance
fuskokin su na kallon kasa. Ya nuna sojoji suna dukan su da bulala kuma suka sa su wanka da shan ruwan kwata.
NAIJ.com ba za ta iya tabbtar da inganci
tushen bidiyon ba, mai Magana da yawun
sojoji Brigediya Janar Sani Usman, yace
manyan jam’ian sojoji sun san da bidiyon.

Ya fada ma manema labaru a daren Laraba cewa “A sane muke da bidiyon.”

“Mun samu labarin bidiyon, kuma mun sa a
fara binciken al’amarin, zamu bayyana ma
al’umma sakamakon binciken.”

“Manjo janar Abubakar Adamu mai kula da
rudunar 82 Division, ke jagoranatar binciken bidiyo kuma za’a bayyana ma al’umma sakamakon binciken.”
Inji shi

To mudai saidai muce Allah ya kyauta "duk wanda baiji bariba yaji hoho da sannu sannu dan kuka ke jawowa uwarsa jifa"
No comments:
Write Comments