Tuesday

Home “Wa ya kashe "yar aduwa : munaso ayi cikakken bincike”: sen. Shehu sani
Yar’Adua ya rasu a ranar Litinin 5 ga watan Mayu, 2010 bayan dogon jinya
- Amma Sani ya bayyana cewa sabon labarin da ya zo kwanan nan ya nuna cewa mutuwar Yar’Adua ban a Allah bane Sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari dabude sabon bincike a kan mutuwar marigayi shugaban kasa Umar Yar’Adua. NAIJ.com ta tattaro cewa Sanata Shehu Sani ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa Buhari ya tabbatar anyi binciken ainahin dalilin mutuwar Yar’Adua ba tare da bata lokaci ba. Yace: “Da wannan sabon hujja da ya billo game da mutuwar Yar’Adua, shugaban kasa Buhari ya bude sabon binciki cikin ainahin abunda ya faru da marigayin shugaban kasar. “Kafin yanzu a yarda cewa mutuwar tasa daga Allah ne, bayan dogon rashin lafiya, hujojin kwanan nan sun tabbatar da sabanin haka. Dole mu fayyace tarihin kwado. Me ya kashe shugaban kasa Umaru Yar’Adua sannan wa ya kashe Umaru Yar’Adua?
No comments:
Write Comments