Monday

Home › › Wanda ya kafa kungiyan MASSOB yace "Nasan wadanda suka dauki hayar Nnamdi kanu."

Wanda ya kafa kungiyan neman yancin yan
asalin Biyafara, IPOB, Ralph Uwazuruike, ya zargi gwamnatin jam’iyyar All Progressive Congress, APC da ba shugaban IPOB Nnamdi Kanu makudan kudaden dan kawo ma fafitukar da suke yi cikas.
Uwazuruike yayi wannan furucin ne a
lokacin da yake zantawa da yan jarida.Ya ce kokarin da yake yi na samar da Biyafara, “ta hanyar zaman lafiya” ya samu tangarda ta dalilin Kanu wanda “jami’an tsaro suke amfani dashi wajen kawo karshen gwagwarmayar su.

Wanda ya kafa kungiyan MASSOB yace
shugaban IPOB ya zo ne dan ya rusa
gwagwarmayar su na samar da Biyafara,
kuma zai fara ne ta hanyan hana zaben
Anamabara da za’ayi 18 ga watan Satumba,
wanda yace kada kowa ya fito kada zabe.

Ya ce Belin da aka bashi “yaudara ce kawai, ”
Uwazuruike yana mamakin cewa tun da aka
sako Kanu bayan ambashi beli sabdoda rashin lafiya bai ziyarci kowani asibiti ba.”

Ya kara da cewa ,“Nnamdi Kanu yana yaki da yan Biyafar ne kawai. Kuma jami’an tsaro suna amfani da shi.
Sun tunkare shi ne bayan "Sun ji shi yana
kururuwa a radiyon Biyafara kuma ya amince da yin aiki da su.”
“Babu zabe a jihar Anambara, yunkurin ne na jam’iyyar APC wajen kawo karshen
gwamnatin Obiano ta hanyan kawo rudani a
jihar" wannan shine abun dake faruwa, kuma jami’an tsaro ne suka hada wannan wajen amfani da Kanu.
“Nasan manyan gidajen da Nnamdi Kanu da
ire-iren sa suke da shi a kasashenn waje.
Kanu ya cigaba da kunyatar da kanshi Kaman yadda yake yi yanzu , saboda wasu daukan nauyin sa, kuma nasan masu daukan nauyinsa.”
No comments:
Write Comments