Wednesday

Home › › Wani dan sanda ya kashe kansa saboda an canja masa gurin aiki zuwa Maiduguri

Wani dan sandan Najeriya a Abakaliki babban birnin jihar Ebonyi da aka bayyana sunansa da Donatus Oyibe ya kashe kansa sakamakon samun sanarwar an sauya masa gurin aiki zuwa Maiduguri babban birnin jihar Borno.
An bayyana cewa, Oyibe dan yankin Ndegu Ishieke na karamar hukumar Ebonye ya fada rijiya adaren Lahadin da ta gabata bayan ya shaida wa iyalinsa cewa, ya tafi diban ruwa.
Al’umar yankin sun ce, ya shiga wani yanayi tun ranar 24 ga watan Agusta da aka aika masa da takardar sauyin gurin aiki zuwa birnin Maidugurin jihar Borno.
Majiyoyin ‘yan sanda sun ce, yana cikin rukunin ‘yan sandan kwantar da tarzoma da aka dauka daga bataliya ta 32 da ke Abakaliki aka tura Maiduguri.

An bayyana mutuwar tasa da alaka da sauyin gurin aikin da aka yi masa.
‘Yar marigayin Ukamaka ta bayyana cewa, mahaifinta ya dauki bokiti tare da tafiya diban ruwa a wata riji da daddare wanda suka ga bayan awanni bai dawo ba sai suka shiga neman sa.
Ta ce, a lokacin da suka isa bakin rijiyar sai suka bokitin amma ba su ga baban nata ba amma daga baya sai suka gan shi a cikin rijiyar ba rai.
($ource=trt hausa)
No comments:
Write Comments