Friday

Home Yadda Jonathan yaci amanar musulunci A shekarar 2014

A ranar 31-December-2014 akayi taro
da ya shafi tsaro na "United Nations
Security Council" wanda shugaba
Buhari yakeyin irinsa a yau Talata 19-
September-2017.

Wancan taron, an tsara za'ayi kuri'ane
tsakanin kasashe 15 da ake kira "15-
member security council".

Wannan kuri'a kuwa za'ayi ta ne domin tabbatar da wasu abubuwa kamar haka: da
farko dai, kasar Musulmai ta Palestine
wacce kasar Yahudawan Israel ke
zalumta, an fitar mata da wasu
abubuwa kamar haka--wanda kuma
dukkan kasashen larabawa suka yarda
akai--cewar, za'a samu watanni 12
domin tsagaita wuta na rikici tsakanin
Palestine da Israel, a cikin watanni 12
nan, za'a fara shirye-shirye don
tabbatar da halastacciyar kasar
Palestine harma da basu East
Jerusalem a matsayin babbar helkwata
na kasarsu, sannan a cikin wadannan
watannin dukkan sojojin kasar Isreal da
suka mamaye yankunan Palestine za su
fita su janye dakarunsu, duka cikin
watanni 12 din can har zuwa wa'adi na
karshe a shekarar 2017 din nan, daga
nan ba za'a sake ganin sojojin Isreal a
kasar Palestine ba balle su yi ta kashe
yara da matansu da zalumtar
musulman Palestine, sannan har yanzu
kuma, da tabbatar da cewar yan gudun
hijira na Palestine da suke kasar Israel
su ma za'a basu damar komawa
gidajensu lafiya kalau. Wadannan
dukansu na cikin abinda waccar kuri'a
za ta tabbatar.

Ga yadda aka tsara abin, idan Palestine
ta samu kuri'ar kasashe 9 cikin 15 suka
goyi baya, to za'a tabbatarwa da
Palestine wadancan muradun nata
duka, daga nan za su fita cikin takura,
zalunci, da ketare iyaka irinnan
Yahudawan Israel.

Nigeria ta kasance a koda yaushe tana
goyon bayan duk wani abu da ya shafi
Palestine, don haka ma ake ganin
cewar Nigeria za ta shiga sahun masu
goyon baya a wancan karon.

Ana haka, sai Palestine ta samu goyon
bayan kasashe 8 dukansu sun mara
mata baya, sun hada da, China, France,
Russia, Argentina, Chad, Chile, Jordan
da kuma Luxemburg. Nigeria ce ta 9
wajen kada kuri'a, don haka yan
Palestine sun fara murna domin ganin
irin yadda Nigeria ke goya musu baya.
Ana haka sai ga jakadan Nigeria a
wajen jefa kuri'ar, Prof. Joy Ogwu, ga
mamakin kowa sai kawai ya goyi bayan
kasashen Britain, Lithuania da kuma
Republic of Korea da Rwanda wajen
nuna rashin amincewa, Australia da
United States su ma suka nuna rashin
amincewarsu, shikenan wancan kudirin
ya bi iska. Yanzu Palasdinawa za su ci
gaba da bauta wa Yahudawan Isra'ila,
za'a ci gaba da yiwa matansu fyade,
kashe yaransu kanana, rushe gidajensu,
da kuma tabbatar da su a matsayin
"haramtacciyar kasa".

Bayan wannan zaben, sai ga Prime
Minister na kasar Israel, Benjamin
Netanyahu na cewa: "Ina mika godiyata
ga Amurka da Australia sannan da
godiya ta musamman ga shugaban
kaasar Rwanda, abokina Paul Kagame,
da kuma shugaban kasar Nigeria,
abokina Goodluck Jonathan".

Da aka tambaye shi yaya akayi Isra'ila
ta ci nasara, sai yace: "Na yi magana
da su biyun (Kagame da Jonathan)
kuma suka min alkawarin cewar ba za
su goyi bayan wannan kudurin ba, kuma
sun ciki alkawarinsu". Inji Netanyahu.
Shi kuma jakadan Palestine a Nigeria,
Montaser Abuzaid cewa yayi: "kasarsa
da mutanensa sun ji matukar bakin ciki
da mamaki ta yadda Nigeria ta juya
musu baya. Muna girmama Nigeria
sosai saboda Nigeria na daya daga
cikin kasashen farko da suka tabbatar
da halastacciyar kasar Palatine tun
shekarar 1988, kuma ta kasance tana
goyon bayanmu tun wancan lokacin,
amma abinda ta mana jiya ya kadamu".
Sannan ya sake cewar, sai da ya kira
Ministan Harkokin Waje na Nigeria ya
tambayeshi ko za su goyi bayansu, ya
tabbatar masa da cewar za su goyi
bayansu, anyi haka jiya kawai sai ya
wayi gari yau wai ya ji Nigeria ta juya
musu baya.

Daman an zargi Goodluck Jonathan
ganin cewar a "UN General Assembly"
an ganshi ya ware da Prime Minister na
Israel, Benjamin Netanyahu, Secretary
of State na Amurka Hillary Clinton,
Minster na tsaron kasar Israel Ehud
Barak, wanda ake ganin zamansu ne ya
chanja alkiblar Nigeria akan
Palasdinawa.

Yau gashi yan'uwanmu Palasdinawa
suna cikin halinda suke ciki na tashin
hankali, rashin tsaro, rashin zaman
lafiya da muzgunawa a dalilin hukuncin
mutum daya: Goodluck Jonathan. Yau
Palasdinawa za su iya cewar suna
halinda suke cikine a dalilin Nigeria,
tunda a wancan lokacin Nigeria ta samu
damar chanja alkiblarsu.

ALLAH YA ISA TSAKANINMU DA
JONATHAN, ALLAH KA YI MANA
MAGANINSA KA MASA ABINDA YA
MANA.

Wannan labarin na fassara ma'anarsa
ne daga littafin siyasar nan na Olusegun
Adeniyi mai suna "AGAINST THE RUN
OF PLAY -- how an incumbent
president was defeated".

Daga shafuka na 166-168. Shi ya kawo labarin, da kuma wasu labarun sosai akan siyasar Nigeria da kuma abubuwan da suka
faru a lokacin Jonathan irin wadannan
da kuma irinsu Boko Haram, Chibok da
abubuwa da yawa.

No comments:
Write Comments