Tuesday

Home Zainab indomie :“Har yanzu ban fidda ran dawowa harkar fim ba.”
Shaharraiyar jarumar wadda a yanzu haka tauraruwar ta ta riga ta dishe ta bayyana cewa tana nan tana murmurewa tana kuma kara kammala shire-shiren ta domin ta dawo da karfin ta ta kuma disashe taurarin wasu jaruman a harkar yanzu. Naij.com dai ta samu cewa a kwanakin baya anyi ta rade-raden cewa jarumar tana fama da wata matsanaciyar rashin lafiya ne da kuma ta ke hana ta walwala da harkokin nata kamar yadda ta saba. Haka ma dai a baya jarumar ta fito a kafafen sadarwar zamani inda tayi tofin Allah-tsine ta kuma sha alwashin yi wa duk wanda ya kara cewa tana fama da kanjamau Allah ya isa.
No comments:
Write Comments