Sunday

Home › › Jerin Sunayen "yan wasan Hausa Masu Marawa Atiku Baya A 2019 : ciki harda A. Zango

Mun samu labari daga Abu Sidiqu cewa wasu 'Yan wasan fim sun yi wani taro a Garin Kaduna inda har su ka nuna alamun marawa Alhaji Atiku Abubakar baya a zabe mai zuwa.

'Yan wasan fim na Kannywood na marawa
Atiku baya bisa dukkan alamu. Irin su Fati Muhammad su ka halarci taron inda aka kara mata girma a harkar. Sauran manyan Taurari irin su Adam Zango da Rabiu Rikadawa da wasu Darektoci ma ba a bar su a baya ba.

Sauran wadanda su ka halarci taron a
Kaduna sun hada da Abida Mohammed da
Fati Washa, Sadiya Gele, Tahir I. Tahir, Shamsu Cash Money, Abbas Sadik, Mama Binta, Binta Kofarsoro, Fati Yola, Fati Mama, Hadiza Kabara, Fati K.K., da dai sauran su.

Ana tunani Wazirin Adamawa Atiku
Abubakar zai tsaya takarar Shugabanci a
2019. Kuma da alamu a wajen taron da aka karrama Fati Muhammad sun nuna goyon bayan su ga tsohon Mataimakin Shugabankasar Alhaji Atiku Abubakar.
No comments:
Write Comments