Saturday

Home › › Mijina Ya Bani Izinin In Koma Sana'ar Film — Inji Fati Ladan
Tsohuwar Shahararriyar jarumar Film ta masana'antar shirya fina finai ta Kannywood wato Fati Ladan ta fito ta bayyana wa duniya cewa babu wani aibu a cikin zaman aure da kuma sana'ar film don kuwa abi mai yiwuwa.

Fati dai tayi sunane a wasu fina finai da tayi a masana'antar Kannywood wanda ya hada da "Ni Dake Mun Dace" kafin tayi aure inda tace bayan tayi auren ma sai da mijinta ya bata sharawa cewa ta koma sana'arta ta film amma taki amincewa.

Jarumar ta bayyana cewa yanzu haka tana gidan mijin ta inda take samun jindadi da kwanciyyar hankali kuma tana zaune lafiya da mijinta babu abinda yake hadasu.

Haka ma dai jarumar ta bayyana cewa yanzu haka dai ta koma makaranta inda tuni ma har ta kai aji uku a jami'a wajen koyon kimiyyar siyasa kuma tana sana'ar ta ta kiwon kifaye da kaji.
No comments:
Write Comments