Thursday

Home › › Almajiran Zakzaky sun kai karar Shugaba Buhari zuwa majalisar dinkin duniya
'Yan shi'a Almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky na
Zariya sun maka gwamnatin Najeriya karkashin
jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari zuwa ga
majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashen
yammacin Afrika da ma kotun duniya ta kasa-da-
kasa suna karar sa game da cigaba da tsare
jagoran su da yake yi.

Shugaban kwamitin fafutukar ganin ankwato
Malam Zakzaky din Sheikh Abdulhamid Bello
ne dai ya sanar da hakan a garin Kaduna a
yayin wat fira da yayi da manema labarai
game da lamarin.
Almajiran Zakzaky sun kai karar Shugaba Buhari zuwa
majalisar dinkin duniya

haka zalika majiyarmu ta samu cewa kuma
Sheikh Bello din ya bukaci gwamnatin
tarayya da ta basu gawarwakin 'yan uwan su
da sojoji suka kashe suka kuma turbude har
347 domin suyi masu sutura su rufe su a bisa
tsarin addinin su.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa a karshen
sherar 2015 ne dai aka yi wata kazamar
arangama tsakanin yan shi'ar da kuma
tawagar jami'an tsaro a garin Zariya inda
yayi sanadiyyar mummunan rikicin da ya
lakume daruruwan rayuka tare da kama
shugaban na 'yan shi'a.
No comments:
Write Comments