Thursday

Home › › Bilyaminu ya gamu da abun da ya kamace shi don shi mayaudari ne - inji kawar Matar shiRahotanni sun kawo cewa daya daga cikin
kawayen Maryam Sanda, matar da ake zargi da
kashe mijinta Bilyaminu dan tsohon shugaban
jam’iyyar PDP ta mara ma kawar tata baya akan
zargin da ake mata.

Bisa ga wani rubutu da kawai mai suna
Maryam Aliyu ta wallafa a shafinta na
Facebook ta nuna goyon bayan ta ga Sanda
dari bisa dari.
Ta kuma kalubalanci mutane da su daina
zargin kawar ta da aikata laifin da ake
tuhumarta a kai.
Majiyarmu ta Pulse Hausa ta rahoto inda
kawar wacce ake tuhuma ke cewa:

“Bilyaminu Kasurgumin mayaudari ne kuma
ya gamu da abun da ya kamace shi.
“Mutane na ta kumfar baki akan al'amarin
Bilyaminu da Maryam ba tare da sanin
gaskiyar abun da ya faru ba.
"Babu wata kwakwarar shaida mai nuna cewa
ita ta aikata laifi. Abun da na sani shine shi
dai kasurgumin mayaudari ne kuma a ra'ayi
na ya gamu da abun da ya kamace shi.
“Idan ma Maryam ta kashe shi wanda na san
ba haka bane, ai tayi dai dai domin yana
yaudarar ta da bin mata ba tare da ta sani ba.

“Ni dai na tsaya a bangare mai cewa ya mutu
ne a lokacin da suke rigama amma ba wai a ce
ta kashe shi da hannun ta ba. Ki cigaba da
juriya Maryam, Allah yana tare da ke."
Kamar
yadda ta wallafa a shafinta.
No comments:
Write Comments