Friday

Home › › Dalilin da yasa Buhari ba zai iya cika dukkan alkawiran da ya dauka ba - Oyegun
John Odigie-Oyegun wanda ya kasance
shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa ya bayyana cewa alkawaran zabe da jam’iyyar ta dauka sun kasance kudiri.

A cewar rahoto, shugaban na APC yayi
magana a lokacin taron gabatar da littafin kokarin gwamnatin shugaban kasa
Muhammadu Buhari, mai taken: ‘Making
Steady, Sustainable Progress for Nigeria’s Peace and Prosperity’.

Oyegun yace wasu mutane na da fadin cewa
jam’iyyar ta ki aiwatar da wasu daga cikin alkawaranta amma yayi bayanin cewa
yayinda aka cimma wasu, sauran na bukatan
tsare-tsare na dogon lokaci.

A ranar Alhamis, 16 ga watan
Nuwamba, shugaban kasa Buhari yace ya
yanke shawarar biyan alkhairi da yan
Najeriya sukayi masa a lokacin gwagwarmayan da ya sha na jinya ta hanyar
kare ra’ayinsu da dukkan karfi a kalkashinsa.

Punch ta ruwaito cewa ya jaddadda cewa
gwamnatinsa ta jajirce domin inganta tsaro, yaki da cin hanci da rashawa da kuma sake fasalin tattalin arziki.
No comments:
Write Comments