Wednesday

Home › › Dalilin da yasa har yanzu ake damawa da Tinubu a siyasar Najeriya – Inji sarkin Legas
Oba na Legas, Rilwan Akiolu ya bayyana
dalilin da yasa jigon jam’iyya mai mulki ta
APC, Bola Tinubu, har yanzu yana da matsayi
a harkokin siyasa a Najeriya.


Sarkin ya ce takunsa ya sanya shi tsawon
lokaci a siyasar Najeriya Najeriya.
Da yake jawabi a Ibadan, babban birnin
jihar Oyo a ranar Talata, 21 ga watan
Nuwamba, Akiolu ya ce, "Jarumtakar Tinubu
ya sanya shi a matsayin da yake a yau a
lokacin da babban jam’iyyar adawa ta PDP ta
matsa wa yankin kudu maso yammacin kasar
lamba".

majiyarmu ta tattaro cewa, sarkin, wanda ya
yaba wa Tinubu game da kokarinsa na gina
Legas, ya kuma bayyana cewa ba za a iya
kwace jihar a hannun APC ba.

Har ila yau, sarki ya yaba da ayyukan
gwamna Akinwunmi Ambode na jihar Legas.
"Ba na ɓoye zuciyata, babu wanda zai iya
kwace Legas a hannun APC. A tarayya kuma
ya kamata mu hada karfin mu waje daya" , inji
shi.
No comments:
Write Comments