Friday

Home › › Hanyoyi 5 da za ku kula da kan ku cikin lokacin hunturun sanyi.
Wadannan hanyoyin guda biyar ya zama lallai kusansu domin kare jikkunanku daga illolin sanyi.
1. Sanya kayan sanyi masu nauyi nada
matukar muhimmanci a wannan lokacin
musamman ma ga yara da kuma tsofaffi
domin kare kai.
2. Yana da matukar anfani, mutane su rika
saka tubarau da zai rika rufe masu
idanuwansu da ma hanci da baki a wasu
lokuta domin samun kariya.
3. Yana da kyau mutane su rika shafa mai da
ke da maiko sosai a wannan lokacin domin
samun laushin fata musamman ma a baki da
kuma kafa.
4. Yana da kyau a rika wanke kayan abinci
da ganyayyaki da ma 'ya'yan itatuwa sosai
kafin ci a wannan lokacin.
5. Haka zalika atisaye da motsa jiki yana da
matukar anfani shima domin samun
dumamar jiki da kuzari.
No comments:
Write Comments