Wednesday

Home › › Kotu ta raba tsohon aure na shekaru 22 sakamakon rashin girki akan kari
Wata kotun al'adu dake garin Nyanya a birnin
tarayya Abuja, ta raba auren wasu a ranar
Talatar da ta gaba bayan sun shafe shekaru 22
sakamakon dabi'ar uwargidan ta yin girki sau
guda a mako.

Alkalin kotun Mista Jamilu Jega, ya cika
burin mijin wannan mata Mista Garba
Pakachi, inda ya raba auren da cewar zaman
lafiya ya riga da ya kare a zamantakewar
auren.
Kotu ta raba tsohon aure mai shekaru 22 sakamakon
rashin girki akan kari
Tun a makon da ya gabata Pakachi ya ya
shigar da kara a gaban kotu akan ta raba
auren su na tsawon shekaru 22 akan rashin
yin girki domin cimar yau da gobe.

Alkali Jega ya umarci Garba akan ya dauki
nauyin 'ya'yayen da suka haifa da kuma
umartar shi na biyan Naira 20, 000 a kowane
wata domin kulawa da jaririn su dan
watanni 6 da haihuwa.
Ita kuwa uwargidan Martha, ta kalubalanci
wannan tuhuma, sai dai kuma ta ce ba ta da
wata sha'awa dangane da auren.
No comments:
Write Comments