Thursday

Home › › Yanzu-Yanzu: Hukumar EFCC ta saki tsohon sakataren gwamnatin Jonathan
Hukumar nan dake yaki da masu yiwa tattalin
arzikin kasa zagon kasa watau Economic and
Financial Crimes Commission, EFCC a turance ta
saki tsohon Sakataren gwamnatin tarayya a
karkashin mulkin tsohon shugaban kasa
Goodluck Jonathan mai suna Senata Anyim Pius
Anyim bayan kamashi da tayi.


Mun dai samu cewa hukumar ta EFCC ta
kama tsohon Sakataren Gwamnatin ne bisa
wani binciken da take yi masa da laifin ansar
wasu makudan kudaden da suka kai Naira
miliyan 520 a hannun tsohon mai ba
shugaban kasa Jonathan shawar game da
harkokin tsaro Kanal Sambo Dasuki.

Majiyarmu dai ta samu cewa sauran laifukan
da ake zargin sa da aikatawa sun hada da
bayar da wata kwangiyar Naira Biliyan 13 ga
wani kamfanin da yake da alaka da shi da
hakan kuma ya sabawa dokar kasa.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa mun
ruwaito maku cewa EFCC a kwanan baya ta
garzaya kotu sannan kuma tayi nasarar
samun hurumi daga gareta na cigaba da tsare
tsohon Sakataren gwamnatin tarayya Anyim
Pius Anyim har na zuwa kwanaki 30.
No comments:
Write Comments