Thursday

Home A wannan sabuwar Shekarar ta 2018 ,manhajar whatsapp zata daina aiki akan wasu wayoyi.
kamfanin whatsapp sun sanar da abokan huldarsu cewa manhajarsu zata daina aiki akan wasu wayoyi a wannan sabuwar shekara mai kamawa ta 2018

Kana amfani da Manhajar Whatsapp A wayarka,?? to kayi gaggawar karanta wannan sakon.

Whatsapp zai katse ya daina aiki aksn wasu wayoyi da aka kayyade daga ranar 1-january 2018, Wayoyin da wannan abu ya shafa sun hada da : kowacce waya da take gudana akan Windows 8.0 , BlackBerry Os ko BlackBerry 10.

kamfanin na Whatsapp sun sake sabunta sanarwar tasu wadda suka fitar tun a shekara 2016.

“lokacin da muka kaddamar da Whatsapp a shekarar 2009, mutane suna amfani da wayoyi wadanda zakaga ba irin na yanzu bane. Shi kamfani Apple a lokaci baifi "yan watanni da fara kirkiro wayoyi ba.
kimanin kashi 70 na wayoyin da kamfanin Apple suka sayar a lokacin, operating system nasu anyishi ne aksn BlackBerry da kuma nokia”
a cewar kamfanin

Sauran wayoyin da zasu daina aiki da whatsapp sun hada da Nokia Symbian S40 , Nokia S40 wacce zata daina aiki da whatsapp a 31-12-2018 Da kuma wayoyi kirar android v2.3.7 a 01-02-2020.
No comments:
Write Comments