Friday

Home › › APC reshen Kano ta yi barazanar kai Buhari kara a kotu idan ya ki fitowa takara karo na 2
Mun samu labari daga jaridar Premium
Times cewan a ranar Alhamis, 7 ga watan
Disamba, jam'iyyar APC reshen Kano ta
yarjewa Buhari tsayawa takara karo na 2 a
2019. Ta yi hakan ne bisa la'akari da
ayyukan da ya yi a shekaru biyu da ya yi ya na shugabanci.

Garba Shehu, mai magana da yawun Buhari,
ya ce Buharin bai amince ba kuma bai ki ba.
Sai dai ya yi murmushi ne kawai sannan ya
karkatar da jawabin sa zuwa ga yin kira ga al'ummar Najeriya da su hada kan su.

Shi kuwa Ciyaman din APC reshen Kano,
Inuwa Abbas, ya ce sun yarjewa Buhari
tsayawa takaran ne sakamakon ayyukan sa
na tsaro da yaki da rashawa da karfafawa
matasa da kuma farfado tattalin arziki. Abbas ya ce Buhari ne ya cancanta ya ja ragamar Najeriya musamman a irin wannan lokaci.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewan,
Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, cikin
barkwanci ya ce a shirye su ke su kai Buhari kara kotu don tilasta masa amincewa da tsayawa takarar karo na 2. Ya kuma ce ma su rike madafan ikon da su ka shude ne su ka wawushe asusun gwamnati.

jaridar NAIJ.com ta bada rahoton yadda
Buhari ya roki 'yan Najeriya da su yi hakuri su saurara ma gwamnatin sa. Ya ce al'amurra za su daidaita nan ba da dadewa ba.
No comments:
Write Comments