Sunday

Home › › Ba don Kwankwaso ba da ‘Yan Boko Haram sun kashe Buhari a 2013
Ba don Kwankwaso ba da ‘Yan Boko Haram sun
kashe Buhari a 2013 : cewar Muhd yusuf.

Wani ‘Dan siyasa a Kasar nan mai suna
Muhammad Yusuf wanda ya taba aiki da Tsohon
Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya
bayyana abin da ke tsakanin Kwankwaso da
Buhari da yadda Kwakwaso ya ceci rayuwar
Buhari hannun ‘Yan ta’adda kwanakin baya.
Ba don Kwankwaso ba da ‘Yan Boko Haram sun
kashe Buhari a 2013
Idan ba ku manta ba a 2013 an taba kai hari
inda aka kusa ganin bayan Shugaba Buhari a
Garin Kaduna. Muhamamd Yusuf wanda
kusan dangin sa ‘Yan uwa ne wajen
Shugaban Kasar ya bayyana cewa
Kwankwaso ya ceci tsohon Shugaban a Ranar.

Yusuf yayi wannan rubutu ne kwanakin baya
a Jaridar The Cable inda yace jim kadan
bayan abin ya faru Shugaba Buhari ya kira
Kwankwaso a waya inda yayi masa godiya.
Gwamnan Kano a lokacin ne ya mikawa
Shugaban Kasar kyautar motar da yake ciki.

Abin dai ya zo da sauki don kuwa harsashi
ba ya ratsa motar, ta haka ne Muhammadu
Buhari ya tsira a wannan rana. Daga baya
dai Rabiu Kwankwaso ya taka mota domin
gaida Buhari bayan hadarin. Da dama dai ba
su san abin da ya wakana ba a wancan
lokaci.

A cewar Yusuf, wata rana Buhari ya taba
cewa zai so ya ga Kwankwaso ya zama
Shugaban Kasa lokacin da Nduke Obiegbuna
na Jaridar This Day ya tamabaye sa wanda ya
dace da mulkin Najeriya. Sa'an nan Buhari
yace Kwankwaso zai iya gyara Najeriya cikin
kankanin lokaci.
No comments:
Write Comments