Tuesday

Home › › Ba za'a taba iyawa dan Nigeria ba : inji shugaba buhari
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne ya fadi hakan, sakamakon korafin 'yan Najeriya, Ya ce duk wani kokari da za a yi wa dan Najeriya toh ba za'a taba gamsar da shi ba, Sai dai kuma korafin ba zai karya masu gwiwa ba, za su ci gaba da jajircewa.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce, idan a na maganar yaki da rashawa, to ba za'a taba iya gamsar da 'yan Najeriya ba. Ya fadi haka ne yayin zantawa da al'ummar
Najeriya gabanin zaman taron Kungiyoyin
Kasashen Afirika da na Turai (AU-EU), da a ka yi kwanaki 5 da su ka wuce a Kasar Cote d'voire.

Buhari ya yi wannan bayani ne sakamakon
korafin jama'a na cewan a na nuna wariya
da bambanci a yakin. Don haka ne mutane su ke kiran da a canja salon tafiyar, a daina saka siyada fa bambanci a cikin yakin.

Buhari bai tsira daga suka ba a lokacin da ya yaki rashawa a mulkin sa na soja, a yanzun din ma bai tsira ba duk da salon yakin sun sha banban. Don haka ne ya ce sai dai kawai ya yi bakin kokarin sa amma dan Najeriya kuwa, ba za a taba iya masa ba.

Buhari ya yi kuka da yadda a ka ta yin
almubazarranci da kudin Najeriya daga 1999 zuwa 2014, lokacin da gangar man fetur har dala 143 ya taba kaiwa. Ya ce sun samu lamurra sun tabarbare da su ka karbi mulki, ga shi kuma farashin gangan man ya fadi warwas, har zuwa dala 28.

Hakan bai sa sun yi kasa a gwiwa ba, ya ce sun ta fafatawa sun kuma jajirce tare da neman dauki daga wurin Allah. Tsanani da a ka shiga a 2016 ta kai ga ya ji kamar ya yar da shugabancin ya gugu, in ji shi. Ya ce da taimakon Allah, za su ci gaba da kokari wurin cika alkawurran da su ka dauka.
No comments:
Write Comments