Saturday

Home › › Ban taba satar ko sisin kwabo ba a yayin mulki na - Atiku Abubakar
pdp, atiku abubakar, pdp national convention, national convention
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya na farko a wannan jamhuriyar sannan kuma
goggagen dan siysa Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa bai saci ko sisin kwabo ba a lokacin da yayi zamanin mulkin sa a matsayin mataimakin shugaban kasa daga shekara ta 1999 zuwa 2007.

Fitaccen dan siysar dai yayi wannan bayanin ne a cikin wata doguwar wasikar da ya aike zuwa ga wani mai wasan barkwanci da aka fi sani da 'I Go Dye' game da zargin da ake yi masa na tara dukiya ta hanyar haram.


ya kuma bayyana masa cewa shi cikakken
attajiri ne tun kafin ya shiga siyasa ko ma a bashi wani mukami a 1999 inda yace a je a duba ya bayyana kadarori na miliyoyin Nairori kafin shigar sa gwamnati.

Haka nan kuma Atiku din ya bayyana yadda
ya taimaki jam'iyyar da kudade da dama na
kambe da kuma yadda yayi anfani da
kamfunnan sa wajen taimakon jam'iyyar tun
lokacin kamfe.
No comments:
Write Comments