Monday

Home › › Dandalin Kannywood: Ainahin tsakani na da Rahma Sadau - Inji Jaruma Nafisa Abdullahi


A wannan karon kuma, jaruma Nafisa Abdullahi ta
fito tayi bayani dalla-dalla game da ainihin
alakar ta da jaruma Rahma Sadau musamman
ma a farfajiyar shirya fina-finan Hausa ta
Kannywood duba da yanayin yadda ake yayata
cewa dangantaka a tsakanin su tayi tsami.
Jarumar dai tayi wannan karin haske ne
yayin wata fira da Weekly Trust jim-kadan
bayan ta amshi kyautar ta ta gwarzuwar
jaruma a fina-finan Afirika a birnin Landan
a kwanan baya inda ta bayyana cewa ita
zaune take lafiya da kowane abokin sana'ar
ta.

NAIJ.com dai ta samu cewar da aka tambaye
ta ko da gaske ne ba su ga-maciji da junan su
ita da korarrar jarumar nan Rahama Sadau,
sai ta kada baki tace ita dai gaskiya wannan zargin ba gaskiya bane don kuwa babu wani
tsabani a tsakanin su yanzu.
Jarumar ta kuma bayyana cewa ita Rahma
Sadau kanwa ce a wurin ta sannan kuma
dukkan su suna yin aiki ne a karkashin
kamfani daya don haka ba gaskiya bane ace
kuma suna fada da junan su.
No comments:
Write Comments