Saturday

Home Dandalin Kannywood: Jerin Fina-finai 5 da kar ka sake a baka labari
A sakamakon gabatowar karshen shekarar 2017,
a yau dandalin na Kannywood ya kawo muku
jerin fina-finai 5 da suka yi fice wajen shahara ta
fuskar nishadantar wa da kuma debe kewa
wanda bai kamata a ce sun wuce bamu ganewa
idanun mu ba.

NAIJ.com ta kawo muku jerin fina-finai biyar
na Kannywood da suka zamto zakarun
gwajin dafi a shekarar 2017 da ya zamto
kusan wajibi akan mu da mu arasa musu
lokutan mu.

Gwaska return.
gwaska return hausa film movie
wannan shima sabon film ne da kamfanin kannywood zai fitar a sabuwar shekara mai kamawa 1-1-2018.


1 - Kalen Dangi
Wannan shiri ya kunshi soyayya, daukaka da
daraja, karya tare da cin amana, inda
jarumai irin su Ali Nuhu, Aminu Momo, Fati
Washa da Sadiq Sani Sadiq suka nuna
gogewar su da kwarewa.

2. Mansoor.

Wannan shirin yayi matukar shahara a
shekarar nan ta 2017, inda batutuwan sa ke
ci gaba da gudana a bakunan al'umma,
wanda ya malalo yadda wasu daliban
makaranta suka shaku da juna sai dai kash
azzalumai da 'yan bakin ciki suka kafa musu
kahon zuka.
Jaruman wannan shiri sun hadar da; Ali
Nuhu, Maryam Yahya da kuma Babbale
Hayatu.

3 - Auren Manga
Wannan shiri ya kunshi jarumai irin su
Hadiza Gabon, Suleiman Yahaya da Falalu
Dorayi, inda yayi nazari akan ban dariya da
zai nishadantar da masoya fina-finan hausa.


4-. Rariya.

Wannan shirin na rariya da Yaseen Auwal ya
jagoranta yayi nazari ne akan labarai na
daliban makanta ta 'yan mata da ke nuna
yadda rayuwar wadanda suka fito daga
gidaje daban-daban ke kasancewa a
makaranta.
Jaruman wannan shiri sun hadar da; Rahama
Sadau, Ali Nuhu, Hafsat Idris, Maryam Booth,
Fati Washa, Sadik Sani Sadik da makamantan
su.

5-. Safara
Wannan fim din yayi fice wajen buga
misalin da nazarin yadda batun cinikin dan
Adam a Arewa maso gabashin Najeriya.
Jaruman wannan shiri sun hadar da; Aina’u
Ade, Ali Nuhu, Abba El-Mustapha, Ladidi
Fagge, Jamila Nagudu da kuma Isa Isa.
No comments:
Write Comments