Saturday

Home › › Jam'iyyar PDP ta kafa kahon zuka akan Dala Biliyan 1 da gwamnatin APC ta ware don yakar Boko Haram
Jam'iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewa, tabbas
akwai alamar tambaya akan amincewar da
hukumar tattalin arzikin kasa tayi wajen baiwa
gwamnatin APC dala biliyan guda domin ci gaba
da yakar ta'addancin Boko Haram a yankunan
Arewa maso Gabashin kasar nan.

Jam'iyyar ta bayar da wannan sanarwar ne
ta kafa kahon zuka ga jam'iyyar APC da
sanadin sakataren ta, Kola Ologbondiyan,
inda ya bayyana cewa, ya kamata majalisar
zartaswa ta binciki wannan lamari cikin
gaggawa.

NAIJ.com ta fahimci cewa, jam'iyyar tana
kalubalantar gwamnatin shugaba Buhari da
kulla wata makekashiya wajen karbar
wannan kudade domin kuwa sun biyo ta
hanya ne da kundin tsarin mulkin na kasa
bai musu lamuni ba.

Jam'iyyar ta adawa tana kuma bugun kirji na
karbar jagorancin kasar nan a zaben 2019
mai gabatowa, inda take ci gaba da zargin
APC da yunkurin yin sama da fadi da kudin
kasa.

A kalaman sanarwa na jam'iyyar, " muna
goyon bayan yaki da ta'addanci dari bisa dari
kuma muna kara mika jinjina da bayar da
lambar girma ga dakarun dake gaba wajen
dauki ba dadi da ta'addanci.


"Sai dai idan 'yan Najeriya zasu iya tunawa,
gwamnatin APC tayi ikirarin samun galaba da
cin nasara akan yaki da ta'addanci, saboda
haka muna da ja akan wannan adadin kudade
ta nema matukar bata fito ta bayyana mana
gaskiyar lamarin ba."

"Lokutan karairayi da yada farfaganda tuni
sun kama gabansu a kasar nan, 'yan Najeriya
sun san gaskiya, saboda haka dole mu rike
kafar gwamnatin tarayya kafin ta wawushe
kudin al'umma."


Post By ABDULLAHI H-A


No comments:
Write Comments