Friday

Home › › Kwankwaso da mukarraban sa na kan hanyar su ta dawowa gida - Inji kwamitin amintattu na PDP
Shugaban kwamitin amintattu na jam'iyyar
adawa ta PDP watau Chairman of the Board of Trustees (BoT) a turance Sanata Walid jibrin ya bayyana cewa jam'iyyar ta adawa na nan na dakun sauraron dawowar tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da sauran mukarraban sa.

Dokta rabiu musa kwankwasa.

Shi dai Kwankwaso ya bar jam'iyyar ne a
cikin shekara ta 2014 tare da wasu gwamnoni hudu lokacin da rikicin jam'iyyar ta PDP yayikamari.

jaridar NAIJ.com dai ta bayyana Sanata Walid yayi wannan jawabin ne yayin da yake zantawa da manema labarai game da komawar tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar.

Haka ma kuma ya shawarci dukkan 'ya'yan
jam'iyyar da su rungumi zaman lafiya da
kuma sakamakon karshe da za'a fitar bayan
kammala babban taron gangamin da za suyi
a gobe don zabar sabbin shugabannin
jam'iyyar.
No comments:
Write Comments