Sunday

Home › › Rahama sadau ta tsallake Rijiya da baaya.
Shahararriyar jarumar wasan Hausa, Rahama Sadau, ta sha da kyar a hannun wasu daliban jami'ar Umaru Musa dake jihar Katsina.
rahama sadau
Tun farko shugabannin kungiyar daliban jami'ar ne suka gayyaci jarumar domin karramata a ranar Mata ta duniya. Saidai lamarin ya kwacube bayan isowar jarumar harabar taron, Students Centre, dake cikin jami'ar.

Majiyar mu ta bayyana mana cewar jarumar ta iso wurin taron a makare, kuma zamanta keda wuya a teburin manyan baki sai dalibai suka barke da sowa da murnar ganin jarumar. Dalibai da dama sun nufi jarumar domin samun damar daukan hoto da ita, lamarin da ya kai an kasa sarrafa dandazon matasa masoya ga jarumar dake son yin hoton da ita.

Rahoton da muka samu ya tabbatar mana da cewar wasu daga cikin daliban ba iya son daukan hoto ya kai su ga wurin da jarumar ke zaune ba. Majiyar mu ta shaida mana cewar wasu daliban sun so afkawa jarumar ba don jami'an tsaro sun yi gaggawar shiga tsakani ba.
Da kyar jami'an tsaron jami'ar suka yi nasarar raba Rahama Sadau da janjamim masoyan dake ta kokarin kusantar ta da manufa daban-daban.
Babu rahoton samun lahani ko yin wata illa ga jarumar, an fitar da ita lafiya daga harabar jami'ar.
Kokarin Majiyar mu na jin ta bakin Jarumar ko kungiyar daliban jami'ar Umaru Musa yaci tura.

A satin da ya gabata ne jaruma, Rahama Sadau, ta yi bikin murnar zagayowar ranar haihuwar ta a kasar Cyprus.
No comments:
Write Comments