Sunday

Home Shugaba Buhari ya fara neman wanda zai maye gurbin Ibrahim Magu.
Mu na jin kishin-kishin din cewa Gwamnatin
Shugaba Buhari ta ga uwar barin da ta sa
dole za ta maye gurbin Ibrahim Magu da
wani dabam a matsayin Shugaban Hukumar
EFCC na Kasar. Hakan zai kawo karshen sa-
in-sar sa da Sanatoci.

Uwar bari daga Sanatocin Najeriya ta sa za a maye
gurbin Magu?

Akwai rade-radin da ke yawo a Kasar cewa
Shugaba Buhari ya fara neman wanda zai
maye gurbin Ibrahim Magu a matsayin
Shugaban Hukumar EFCC mai yaki da masu
yi wa tattalin arzikin Kasa zagon kasa nan da
wani ‘dan lokaci.

Shugaban Kasar zai sauya Mukaddashin
Shugaban Hukumar ne da zarar an dawo
hutun Kirismeti. Kafin a tafi hutun dai
Majalisar Dattawa ta kara tabbatar da cewa
wa’adin Magu a matsayin Mukaddashin
Hukumar ya kare.

Ana sa rai Shugaba Buhari ya nada
Mataimakin Kwamishina ‘Yan Sandan Jihar
Kaduna Ahmed Abdulrahman ya zama sabon
Shugaban Hukumar. Rahotanni sun nuna
cewa ba za a samu matsala a Majalisa da
Abdulrahman ba.

Idan ba a manta ba tun a shekarar 2015
Magu yake zama a matsayin rikon-kwarya
bayan da Sanatoci su ka ki amicewa da shi
har sau biyu a Majalisa. Sai dai ba mu da
sahihancin wannan rahoton da ke yawo.
No comments:
Write Comments