Sunday

Home › › Shugaban Kasa Buhari yayi wani jawabi mai ratsa zuciya a Kano.
"Babu abin da ke sosa mani rai kamar
in ga yara sun fito gani na – Inji Buhari"
A yayin taron.


Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya
ziyarci Jihar Kano a makon jiya domin
kaddamar da ayyuka da dama na Gwamna
Abdullahi Ganduje inda ya kuma duba wasu
ayyukan da ake yi a Jihar.

Shugaban yayi wani jawabi a Rana ta biyu a dakin taro na Jihar Kano inda yace abin da addinin Musulunci ya koya mana shi ne
adalci ko da mutum ba ya son abu, idan ya
zama gaskiya dole ya aikata sannan ya nemi ya taimakon Ubangiji.

Buhari yake cewa babu abin da yake sosa
masa zuciya tun yana yakin neman zabe
kamar ya ga kananan yara sun fito domin
ganin su ga Shugaban na kasa. Yace wani
lokacin sai ya nemi a tsaya a mota domin
gudun a taka su a kan titi.

Shugaba Muhammadu Buhari dai ya nemi
mutanen da su ke wurin wannan taro da su
fadawa Jama’an da su kara hakuri inda yake cewa ko da akwai bambanci, abu daya ne daiya hada kowa. Shugaban Kasar yayi jawabinne da harshen Hausa.


Post By ABDULLAHI H-A


No comments:
Write Comments