Friday

Home › › Trela makare da buhunan shinkafa ta afka wani gida, ta kashe jariri da wasu mutane
trailer ta afka wani gida

Wata babban mota dauke da buhunan
shinkafa 600 ta afkwa cikin wani gida a
garin Nasarawa inda tayi sanadiyar mutuwar wani jariri da mahaifiyar sa da ma wasu al'umma da ke cikin gidan.
Kamar yadda Jaridar Northern City ta
ruwaito, lamarin ya faru ne a ranar Litinin kuma bincike ya nuna cewa shinkafar da trelar ke dauke dashi malakin hukumar agajin gagawa NEMA ne, reshen karamar hukumar Doma da ke Jihar ta Nasarawa.

Trela dauke da shinkafa ta fada wani gida, ta kashe jariri da wasu mutane
Kamar yadda wani ganau ya bayyana,
direban da ake zargin yana cikin maye ne ya fada wa gidajen ne a yayin da yake tafiya a titi. Bayan jaririn da uwar sa da suka rasu,

wata mata mai suna Omo Talatu da rasu, da
wata mata 'yar kabilar Tiv da kuma yaran
motar.

Daya daga cikin gidajen da motar ta afka
mallakin wani mutum ne mai suna Mista
Danjuma Omaku wanda yayi rashin
mahaifiyar sa cikin kwanakin nan, gallibi ma mutanen da hatsarin ya afka masu sun zo masa ta'aziyya ne.

Mista Danjuma yayi kira da gwamnati ta
taimaka masa domin bashi da wani gidan
zama kuma tirelan ta rusa masa dakuna 6 da shaguna da ke gaban gidan. Wasu wanda
suka samu rauni a sakamakon hatsarin suna
karban magani a asiitin Doma da dakin
karban magani da ke Igbabu.
No comments:
Write Comments