Friday

Home › › Wata kungiya ta bukaci gwamnatin tarayya ta dakatar da wasu manyan sarakunan arewa 3


Rahoto daga jaridar New Telegraph yace
al'umman kananan hukumomin Numan,
Demsa da Lamurde da ke Jihar Adamawa sun
bukaci a dakatar da Sarkin Kano; Sanusi
Lamido Sanusi II, Lamidon Adamawa; Dakta
Muhammadu Aliyu Mustapha, da kuma
Sultan na Sakkwato; Alhaji Sa'ad Abubakar
III bisa zargin su da daukan nauyin makiyaya fulani masu kai hari ga al'ummar
su.

NAIJ.com rawaito cewa al'ummar sunyi
wannan kira ne ta bakin shugaban su,
Griffith Kpakai a wani taron kungiyar 'yan Jarida na kasa da aka gudanar a ranar Alhamis.

Shugaban kungiyar ya kara da cewa
sarakunan basu fi karfin hukuma ba, saboda haka ya kamata gwamnati ta dakatar da su kana a gudanar da bincike bisa irin rawar da suka taka wajen hare-haren da fulani makiyaya ke kaiwa al'ummar mu.

Daga karshe kungiyar ta bayyana idan
gwamnati na iya tsawata ma sarakunan
kudu, su ma na arewan bai dace a kyale su
ba. Sun ce irin wannan rikicin da yaki ci yaki cinyewa yana iya barazana ga hadin kan Najeriya.
No comments:
Write Comments