Sunday

Home › › ‘Yan Najeriya da su ka ci bakar wahala a Kasar Libya sun ce ba zu kara barin gida ba
N300,000 aka saida ni a matsayin
Bawa a Kasar Libya – Inji wani ‘Dan
Najeriya

'Yan Najeriya na kashe N600,000 domin zuwa kasarwaje a sace

Tun kwanaki kun ji labari cewa a Kasar
Libya ana saida ‘Yan Najeriya da sauran
bakaken fata a halin yanzu. Wani ‘Dan
Najeriya da ya burma cikin wannan bala’ai
ya bayyana yadda ya kare.

Jaridar Daily Trust ta kawo wani dogon
rahoto inda tayi hira da mutanen Najeriya da dama da su ka shiga Kasar Libya domin
samun alheri amma su ka kare cikin bakar
wahala. A cikin wata guda dai an tsero da
‘Yan Najeriya sama da 1,000 daga Kasar ta
Libya.


Wani Bawan Allah mai suna Harrison Okotie
ya bayyana cewa bayan ya kashe sama da
N600,000 domin a tsallaka da shi zuwa Kasar Italiya sai ya iske cewa ashe an saida shi ne a matsayin Bawa a kan kudi N300,000 a Kasar Libya har sai dai Ubangiji ya ceci sa.

Wannan Matashi da ya bar iyalin sa a gida
domin nemo na abinci yace ana tsare mutane ne ana muzguna masu har sai sun fanshi kan su a kan kudin da ya nunka wanda aka saye su.

Harrison Okotie yace ba zai kara zuwa
wata Kasar Larabawa ba har abada.
Jama’a da dama dai sun bayyana irin
wahalar da su ka sha a ketare. An dai daure wasu ne a gidajen yari na wata da watanni ba tare da wanka ba. Yanzu haka daiGwamnatin Najeriya na kokarin ceto
mutanen Kasar ta da ke Kasar ta Libya.
No comments:
Write Comments