Friday

Home › › Yanayin hazo ya tursasa shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa mahaifarsa, Daura, jihar Katsina cikin mota.Buhari ya dauki hanya ne daga jihar Kano
inda ya kai ziyarar aiki na kwanaki biyu.
Babban mataimakinsa na musamman a
kafofin watsa labarai, Garba Shehu ne ya
bayyana hakan a wata sanarwa da yayi ga
manema labarai a ranar Juma’a.

Shehu yace shugaban kasar wanda ya samu
rakiyan Gwamnoni zuwa Daura, Abdullahi
Umar Ganduje da kuma Ababakar Badaru ya
samu tarba daga Gwamna Aminu Masari na
jihar Katsina da sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk a iyakar jihohin Jigawa da Katsina.
No comments:
Write Comments