Thursday

Home › › Zaben 2019 : Dalilin da yasa Buhari ya ziyarci jihar Ebonyi da Kano - Ezekwesili -

Ezekwesili ta bayyana dalilin da yasa
shugaba Buhari ya ziyarci jihar Ebonyi
da Kano.

Shugaban kungiyar 'BringBack Our Girls'
BBOG, Oby Ezekwesili, ta ce shugaban kasa
Muhammadu Buhari, ya ziyarci jihar Ebonyi
da jihar Kano ne dan fara kamfen din zaben 2019.


Ta kuma karyata ikrarin da shugaba Buhari
yayi, na cewa kuri’un mutanen jihar Kano a zaben 2019 da za a gudanar na shine.

A lokacin da Buhari ya ziyarci jihar Kano a makon da ya gabata, yace yana da tabbacin lashe duka kuri’un jihar Kano, saboda mutanen Kano a aljihun sa su ke.

Ezekwesili ta bayyana dalilin da yasa shugaba Buhari ya ziyarci jihar Ebonyi da Kano Ziyarar da Buhari ya kai wa wadannan
jihohin farganda ce, na fara kamfen din
zaben 2019 da wuri, ba wai dan ya damu da
al’ummar kasar ba.

Oby ta bayyana hakane a shafin ta na tuwita a ranar Laraba.

Ezekwesili ta ce Buhari dan siyasa ne da bai damu da matasan dake tasowa ba.


Post By ABDULLAHI H-A


No comments:
Write Comments