VISIT US ON AREWASOUND.COM


HOTTREND ONLINE :
Music Mp3 - Sabuwar Wakar Hamisu Breaker mai suna - Bazana Manta Maryam Ba.
CHECK NEW PRODUCTS HERE
Hamisu breaker 2020 Album Download Mp3 music

Sammani aa 2020 Album : Download Complete Album (Akwai lokaci)

Umar M Shareef Zeenaru 2020 Official AUDIO+VIDEO

MUSIC: Melery 2020 Song Da Dadi So

Tuesday

Home › › An gano 'tsubbun' da Boko Haram ke yi wajen juya kwakwalen 'yan kunar bakin wake
Wasu majiyoyi a Najeriya sun ce hukumomi sun
gano wasu hanyoyin da kungiyar Boko Haram,
bangaren Abubakar Shekau, take bi wajen cusa
wa yara kanana maza da mata akidar kai hare-
haren kunar bakin wake, da kuma yadda suke bi
wajen kaiwa.

Majiyoyin sun ce sashen kai hare-haren
kunar bakin waken kungiyar Boko Haram
bangaren Shekau shine ake kira "Majmu'at
Tafjir" ko Sashen Fashe-Fashe a Hausa, kuma
yana karkashin jagorancin Musa Abuja, mai
alhakin juya kwakwalwar wadanda zasu kai
harin, da karbo umurnin kai hari kai tsaye
daga Abubakar Shekau.

Daya jigon wannan bangare na Majmu'at
Tafjir kuwa shine Abu Darda, wanda
hukumomin Najeriya suka kama shi a can
baya, amma kuma suka sake shi domin
musanyarsa da 'yan matan Chibok da aka
sako kwanakin baya.

Wadannan bayanai su na daga cikin bayanan
da suka bullo a tambayoyin da ake yi ma
daruruwan 'yan Boko Haram da aka kama,
ko kuma suka mika kawunansu a yayin da
sojojin Najeriya suke ci gaba da kai musu
raraka.

SOURCE @HAUSA.NAIJA.NG
No comments:
Write Comments