Sunday

Home › › Cutar 'Hepatitis' ke hana a dauki matasan Arewa aikin soja - Mansur Dan Ali
Ministan tsaro na Najeriya Alhaji Mansur Dan
Ali, ya bayyana cewa cutar hepatitis wato ciwon
kumburin hanta ita ke dakile cancantar mafi
akasarin matasan Arewa daukar su aikin soja.

A cewar sa, mafi akasarin matasan Arewa da
kokarin neman shiga aikin sojin kasa suna
dauke ne da cutar hepatitis , wanda hakan
yake assasa rashin nasararsu wajen cin ma
burikansu.

Da wannan ne ministan yake janyo hankali
iyaye akan su fara tura 'ya'yansu asibitin
domin yi musu gwajin cutar kafin su nemi
aikin soji.

Ministan ya bayyana hakan ne a yayin da ya
halarci shirin tambayoyi da amsoshi mai
taken Hannu da Yawa" da gidan rediyon
Kaduna ke daukar nauyi, inda yace ana iya
magance cutar.


Ministan tsaro; Mansur Dan Ali

Dan Ali ya kara jaddada kiranshi ga iyayen
yara akan su dauki mataki na neman
magance cutar wadda tana da magani a
matakinta na farko kafin abin yayi kamari.

Yake cewa, duk da cewar cutar tana da
magani amma hukumar dakarun soji ba zata
bayar da aiki ga duk wanda yake dauke da
cutar ba, ya kuma ce a halin yanzu akwai
cutar hawan jini dake neman zama ruwan
dare a cikin matasa.

Ministan ya kara da cewa, ya aika da sako
zuwa ga ministan lafiya dangane da yadda
cutar ke kara yaduwa a cikin al'ummar
Najeriya domin a farga wajen daukar
matakai cikin hanzari.
No comments:
Write Comments