Sunday

Home › › Da Dumi-Dumi : El-Zakzaky a karon farko ya gana da manema labarai
Shugaban kungiyar 'yan Uwa Muslumi wato
Islamic Movement in Nigeria (IMN) wanda da
aka fi sani da Shi'a, Sheikh Ibrahim El-
Zakzaky, a karo na farko ya gana da manema
labarai tun bayan da jami’an tsaro suka
kama shi.

Idan dai baku manta rundunar sojin Najeriya
ce ta kama Sheikh El-Zakzaky a watan
Disambar shekarar 2015 a garin Zaria da ke
jihar Kaduna, bayan wani rikici tsakani
‘ya’yan kungiyar da sojoji wanda ta yi
sanadiyar lalata gidansa.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, a wata
sanarwa da kafar watsa labarai ta PR Nigeria
ta fitar, ta ce shugaban kungiyar ya yi
magana da 'yan jarida.

Shugaban kungiyar 'yan Shi'a, Sheikh Ibrahim El-
Zakzaky.

A sanarwar, an turo da hotunansa a yayin da
yake ganawa da manema labarai.

A wata rahoto kuma gidan talbijin na
Channels ita ma ta ce Malamin ya bayyana
cewa yana nan a raye kuma yana cikin
koshin lafiya.

No comments:
Write Comments