Saturday

Home › › Dandalin Kannywood: Dalilin da yasa nayi ma Umma Shehu Tambaya akan addini - Aminu Momo
Shahararren jarumin fina-finan Kannywood
Aminu Sheriff, wato Momoh ya wanke kansa
daga zargin da ake yi masa cewa ya tozarta wata
'yar fim a shirin nasa lokacin da ya yi mata
tambayar da ake gani ba ta shafi harkar fim ba.

A cewarsa, ya yi wa Umma Shehu tambaya
kan addinin Musulinci ne bayan ta bayyana
masa cewa ba ta damu da kallon fina-finai ba
saboda tana zuwa makaranta.

NAIJ.com dai haka zalika ta samu cewa
Aminu Sheriff, wanda ya soma fim sama da
shekara 20 da suka wuce, ya fara ne da
rubuta fina-finai kafin ya soma fitowa a
matsayin jarumi.
Ya rubuta fina-finai irinsu Mugun Nufi, A yi
dai Mu Gani da Dr Gulam.
Fim din da ya soma fitowa a ciki shi ne 'Al-
Mustapha' wanda suka fito tare da fitaccen
jarumi Alhaji Kabiru Maikaba.
No comments:
Write Comments